Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 27:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Dawuda yakan fita da mutanensa su kai wa Geshurawa, da Girziyawa, da Amalekawa hari. Waɗannan su ne mazaunan ƙasar a dā, tun daga Shur har zuwa ƙasar Masar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Dawuda da mutanensa suka haura suka yaƙi Geshurawa, da Girziyawa, da Amalekawa. (Waɗannan su ne mazaunan ƙasar a dā, tun daga Shur har zuwa ƙasar Masar.)

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 27:8
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Wannan ita ce ƙasar da ta ragu, dukan ƙasar Filistiyawa, da ta Geshuriyawa,


Duk da haka jama'ar Isra'ila ba su kori Geshuriyawa, da Ma'akatiyawa ba, amma suka yi zamansu tare da Isra'ilawa har wa yau.


Mutanen Ifraimu kuma ba su kori Kan'aniyawan da suke zaune cikin Gezer ba, amma Kan'aniyawa suka yi zamansu a Gezer tare da su.


Amma ba su kori Kan'aniyawa da suke zaune a Gezer ba, don haka Kan'aniyawa ka zauna tare da Ifraimawa har wa yau, amma Kan'aniyawa suka zama bayi masu yin aikin dole.


Amma sai Geshur da Aram suka ƙwace garuruwan Hawwotyayir ɗin daga gare su, har da Kenat da ƙauyukanta, garuruwa sittin. Duk waɗannan su ne zuriyar Makir mahaifin Gileyad.


Gama na yi wa'adi sa'ad da nake zaune a Geshur ta Suriya. Na yi wa'adi cewa, ‘Idan dai Ubangiji ya komar da ni Urushalima zan bauta masa.’ ”


Absalom ya ce wa Yowab, “Har sau biyu na aika maka domin ka zo in aike ka wurin sarki, ka tambaya mini, ‘Ko me ya sa na komo daga Geshur?’ Da ma ina can har yanzu, ai, da ya fi mini. Yanzu har ni in tafi wurin sarki, idan ina da laifi, to, ya kashe ni.”


Sa'an nan Yowab ya tashi, ya tafi Geshur, ya komo da Absalom Urushalima.


Sa'ad da Dawuda da mutanensa suka koma Ziklag a rana ta uku, sai suka tarar Amalekawa sun riga sun kawo wa Negeb da Ziklag hari. Suka cinye Ziklag, suka ƙone ta.


Amalekawa suka zo su yi yaƙi da Isra'ilawa a Refidim.


Musa kuwa ya bi da Isra'ilawa daga Bahar Maliya, suka shiga jejin Sur. Suka yi tafiya kwana uku cikin jejin, ba su sami ruwa ba.


Ya mallaki Dutsen Harmon, da Salka, da dukan Bashan, har zuwa iyakar Geshuriyawa, da Ma'akatiyawa, da rabin Gileyad, zuwa kan iyakar ƙasar Sihon, Sarkin Heshbon.


Akish kuwa ya kira Dawuda, ya ce masa, “Kai amintacce ne a ganina, daidai ne kuma ka tafi yaƙi tare da ni, gama ban same ka da wani laifi ba tun daga ranar zuwanka wurina har yau, duk da haka sarakunan ba su amince da kai ba.


Abigail, matar marigayi, Nabal Bakarmele, ta haifa masa ɗansa na biyu, Kileyab. Ma'aka 'yar Talmai, Sarkin Geshur, ta haifa masa ɗansa na uku, Absalom.


Sai ga barorin Dawuda da Yowab sun komo daga hari. Sun kawo ganima mai yawa. Abner kuwa ya riga ya tafi, gama Dawuda ya riga ya sallame shi, ya tafi lafiya.


wato azurfa da zinariya na Edomawa, da na Mowabawa, da na Ammonawa, da na Filistiyawa, da na Amalekawa, da ganimar Hadadezer ɗan Rehob, Sarkin Zoba.


Amalekawa suna zaune a Negeb, Hittiyawa kuwa, da Yebusiyawa, da Amoriyawa suna zaune a ƙasar tuddai, Kan'aniyawa suna zaune kusa da teku, da kuma kusa da Kogin Urdun.”


Sai Amalekawa da Kan'aniyawa, mazauna a kan tudun, suka gangaro, suka ci su, suka runtume su har Harma, wato hallakarwa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ