Sa'an nan Saul ya ce, “Na yi laifi, ka komo, ɗana Dawuda, ba zan yi maka kome ba, gama raina ya zama da daraja a gare ka kyau. Na yi aikin wauta, na yi laifi da yawa.”
Dawuda da mutanensa da iyalansu suka zauna tare da Akish a Gat. Dawuda yana tare da matansa biyu, Ahinowam Bayezreyeliya, da Abigail Bakarmeliya, wadda Nabal mijinta ya mutu.
Dawuda ya ce wa Akish, “Idan na sami tagomashi a wurinka, ka ba ni wurin zama daga cikin garuruwanka na karkara domin in zauna a can. Gama me zai sa baranka ya zauna tare da kai cikin birni sarauta?”
Dukan fādawansa, da matsaransa, wato dukan Keretiyawa, da dukan Feletiyawa, da dukan Gittiyawa, sojoji ɗari shida waɗanda suka bi Dawuda tun daga Gat suka wuce a gabansa.