Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 27:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Dawuda bai bar mace ko namiji da rai ba, wato da zai kawo labari, a Gat, domin yana gudun kada su faɗi abin da yake yi, su ce, “Ga abin da Dawuda ya yi.” Abin da Dawuda ya yi ta yi ke nan a lokacin da yake zaune a ƙasar Filistiyawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Bai bar a kawo namiji ko mace da rai a Gat ba, gama yana tunani, “Za su ba da sanarwa a kanmu su ce, ‘Ga abin da Dawuda ya yi.’ ” Haka ya yi ta yi dukan rayuwarsa a ƙasar Filistiyawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 27:11
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Jin tsoron mutane tarko ne, amma wanda ya dogara ga Ubangiji za a ɗaukaka shi.


Gaskiya dawwamammiya ce, amma ƙarya ƙurarriya ce.


Dawuda kuwa ya ce wa Abiyata, “A ran nan Doyeg, mutumin Edom, yana wurin, na sani lalle zai faɗa wa Saul. Ni na zama sanadin mutuwar dukan mutanen gidan mahaifinka.


Idan Akish ya tambayi Dawuda, “A ina ka kai hari yau?” Sai ya ce, “Na kai hari a Negeb ta Yahuza, ko Negeb ta Yerameyel, ko Negeb ta Ƙan'aniyawa.”


Akish kuwa ya amince da Dawuda, yana cewa, “Ya mai da kansa abin ƙi ga mutanensa Isra'ilawa, zai zama barana muddin ransa.”


Suka kwashe mata da dukan waɗanda suke ciki manya da ƙanana, suka tafi da su. Ba su kashe kowa ba, amma suka kwashe su, suka tafi.


Kashegari bayan da an kashe Gedaliya, tun kafin wani ya sani,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ