1 Samaʼila 26:19 - Littafi Mai Tsarki19 Bari sarki ya kasa kunne ga maganar baransa. Idan Ubangiji ne ya kuta ka ka yi gāba da ni, to, bari ya karɓi hadaya, amma idan mutane ne, to, bari su zama la'anannu, gama sun kore ni don kada in sami rabo cikin gādon Ubangiji, suna cewa, ‘Tafi ka bauta wa alloli.’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202019 To, bari ranka yă daɗe, sarkina yă kasa kunne yă ji abin da zan faɗa. Idan Ubangiji ne ya sa ka yi fushi da ni, bari yă karɓi hadaya ta hatsi. Amma idan mutane ne suka sa ka, bari a la’anta su, Ubangiji ne shaidata. Gama sun kore ni don kada in sami rabo cikin gādon Ubangiji, suna cewa, ‘Ka je ka bauta wa waɗansu alloli.’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |