Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 25:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Tambayi samarinka, za su faɗa maka. Saboda haka ka yarda samarina su sami tagomashi a wurinka, gama yau ranar biki ce. Muna roƙonka ka ba barorinka, da ɗanka, Dawuda abin da za ka iya ba mu.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Ka tambayi bayinka za su kuwa gaya maka. Saboda haka ka yi wa mutanena kirki, gama yau ranar biki ce. Ina roƙonka ka ba wa samarina, wato, bayinka, da ni ɗanka Dawuda, duk abin da kake iya ba su.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 25:8
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yahudawan da suke zaune a ƙauyuka, da karkara, suka mai da rana ta goma sha huɗu ga watan Adar, ranar farin ciki, da biki, da hutu, da ranar aika wa juna da abinci.


Gara ku tsarkake cikin, sa'an nan kome zai tsarkaka a gare ku.


Ka raba abin da yake hannunka ga mutum bakwai ko takwas, gama ba ka san irin masifar da za ta auka wa duniya ba.


Su ne ranakun da Yahudawa suka sami kuɓuta daga abokan gābansu. A wannan wata ne kuma baƙin cikinsu ya zama farin ciki, makokinsu kuma ya zama hutawa. Sai su maishe su ranakun biki da farin ciki, da aika wa juna da abinci, da kuma ba da kyautai ga matalauta.


Baba, duba, ga shafin rigarka a hannuna. Tun da yake na yanki shafin rigarka ban kuwa kashe ka ba, sai ka sani ba ni da niyyar yi maka mugunta. Ban yi maka laifi ba, ko da yake kana farautar raina.


Ubangiji ya sāke kiran Sama'ila. Sama'ila ya tashi ya tafi wurin Eli, ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.” Amma Eli ya ce, “Ban kira ka ba, ɗana koma ka kwanta.”


Sa'ad da samarin Dawuda suka zo, suka faɗa wa Nabal dukan abin da Dawuda ya ce musu, sai suka dakata.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ