4 Daga cikin jeji, Dawuda ya ji, wai Nabal yana yi wa tumakinsa sausaya,
4 Lokacin da Dawuda yake a jeji, ya ji labari cewa Nabal yana askin tumaki.
Bayan shekara biyu cif, sai Absalom ya sa a yi masa sausayar tumaki a Ba'al-hazor, wadda take kusa da Ifraimu. Ya kuma gayyaci dukan 'yan'uwansa, wato 'yan sarki.
Sa'ad da aka faɗa wa Tamar, aka ce, “Surukinki zai haura zuwa Timna ya yi wa tumakinsa sausaya,”
Sunan mutumin kuwa Nabal, sunan matarsa kuma Abigail, ita haziƙa ce, kyakkyawa, amma mijinta miskili ne, marar mutunci. Shi daga zuriyar Kalibu ne.
sai ya aiki samari goma, ya ce musu, “Ku tafi Karmel wurin Nabal, ku ce ina gaishe shi.