Sarki bai kasa kunne ga jama'ar ba, gama wannan al'amari, Allah ne ya aukar da shi, domin ya cika maganar da ya faɗa wa Yerobowam ɗan Nebat, ta bakin Ahaija Bashilone.
A daren nan, sai mala'ikan Ubangiji ya tafi ya kashe Assuriyawa a sansaninsu, mutum dubu ɗari da dubu tamanin da dubu biyar (185,000). Sa'ad da mutanen Isra'ila suka tashi da sassafe, sai suka ga gawawwakin nan kwance.
Sai Ubangiji ya buge shi da kuturta, ya kuwa zama kuturu har ran da ya rasu. Ya zauna a wani gida a ware. Sai Yotam ɗansa ya zama wakilin gidan, yana kuma mulkin jama'ar ƙasar.
Ku zuba ido, ku gani, idan ya kama hanya zuwa Bet-shemesh, to, shi ne ya kawo mana wannan babbar masifa, amma idan ba haka ba, za mu sani ba shi ne ya buge mu ba, tsautsayi ne kawai.”
Da tsakar dare sai Ubangiji ya karkashe dukan 'ya'yan fari maza a ƙasar Masar, tun daga ɗan farin Fir'auna, wato magajinsa, har zuwa ɗan farin ɗan sarka da yake a kurkuku, har da dukan 'ya'yan fari maza na dabbobi.