Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 25:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Da Abigail ta ga Dawuda, sai ta yi sauri ta sauka daga kan jakin, ta durƙusa gabansa har ƙasa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Da Abigiyel ta ga Dawuda, sai ta gaggauta ta sauka daga kan jaki, ta rusuna a gaban Dawuda da fuskarta har ƙasa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 25:23
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da yaron ya tafi, sai Dawuda ya tashi daga inda ya ɓuya kusa da tarin duwatsun, ya rusuna har sau uku. Sa'an nan suka sumbaci juna, suka yi kuka, amma Dawuda ya fi yi.


Da ta zo wurinsa, ta iza shi ya roƙi mahaifinta saura. Da ta sauka daga kan jakinta, sai Kalibu ya ce mata, “Me kike so?”


Da ta zo wurinsa, ya zuga ta ta roƙi mahaifinta saura. Da ta sauka daga kan jakinta, sai Kalibu ya ce mata, “Me kike so?”


Daga baya kuma Dawuda ya fita daga kogon, ya yi kira, ya ce, “Ya ubangijina, sarki.” Da Saul ya waiwaya, sai Dawuda ya rusuna.


Sai Rut ta rusuna har ƙasa, ta ce masa, “Me ya sa na sami tagomashi a gare ka, har da za ka kula da ni, ni da nake baƙuwa?”


Ta faɗi a ƙafafunsa, ta ce, “Ya shugabana, bari laifin ya zama nawa. Ina roƙonka ka bar baiwarka ta yi magana, ka kuma yarda ka ji maganar baiwarka.


Sai ta rusuna har ƙasa, ta ce, “Ni baranyarsa ce, ina a shirye in wanke ƙafafun barorinsa.”


Kashegari sai ga wani mutum ya zo daga sansanin Saul, da tufafinsa a yayyage, da ƙura kuma a kansa. Da ya zo wurin Dawuda sai ya fāɗi ƙasa, ya yi gaisuwa.


Da aka zo da Mefiboshet, ɗan Jonatan, wato jikan Saul, sai ya rusuna har ƙasa, ya yi gaisuwa. Dawuda ya ce, “Mefiboshet!” Ya amsa, “Ranka ya daɗe, ga baranka.”


Sa'ad da macen nan da ta zo daga Tekowa ta isa gaban sarki, sai ta rusuna har ƙasa don bangirma. Sa'an nan ta ce, “Ya sarki, ka yi taimako.”


Da Ahimawaz ya zo kusa da sarki, ya ce, “Salama!” Sa'an nan ya rusuna a gaban sarki ya sunkuyar da fuska ƙasa, ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka, wanda ya ba da mutanen da suka tayar wa ubangijina, sarki.”


Sa'ad da Dawuda ya tafi wurin Arauna, da Arauna ya ga Dawuda, sai ya fito daga masussukar ya tafi ya fāɗi rub da ciki a gaban Dawuda ya gaishe shi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ