1 Samaʼila 25:1 - Littafi Mai Tsarki1 Sama'ila kuwa ya rasu. Dukan Isra'ilawa suka taru suka yi makoki dominsa. Suka binne shi a gidansa a Rama. Sai Dawuda ya tashi ya tafi jejin Faran. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20201 Sama’ila ya rasu, sai dukan Isra’ila suka taru suka yi makoki saboda shi. Suka binne shi a gidansa a Rama. Sai Dawuda ya gangara zuwa cikin Jejin Faran. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Musa kuwa ya yi biyayya, daga jejin Faran ya aika da waɗannan shugabanni, Shammuwa ɗan Zakkur, daga kabilar Ra'ubainu. Shafat ɗan Hori, daga kabilar Saminu. Kalibu ɗan Yefunne, daga kabilar Yahuza. Igal ɗan Yusufu, daga kabilar Issaka. Hosheya ɗan Nun, daga kabilar Ifraimu. Falti ɗan Rafu, daga kabilar Biliyaminu. Gaddiyel ɗan Sodi, daga kabilar Zabaluna. Gaddi ɗan Susi, daga kabilar Manassa. Ammiyel ɗan Gemalli, daga kabilar Dan. Setur ɗan Maikel, daga kabilar Ashiru. Nabi ɗan Wofsi, daga kabilar Naftali. Geyuwel ɗan Maci, daga kabilar Gad.