Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 24:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Idan mutum ya sami maƙiyinsa, zai bar shi ya tafi lafiya? Ubangiji ya sāka maka saboda alherin da ka yi mini yau.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 In mutum ya sami maƙiyinsa, zai bar shi yă tafi lafiya ba tare da yin masa rauni ba? Ubangiji yă sāka maka, gama ka nuna mini alheri a yau.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 24:19
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji yakan sāka mini, saboda ni adali ne, Yakan sa mini albarka, don ni marar laifi ne.


Sai Saul ya ce wa Dawuda, “Ubangiji ya sa maka albarka, ɗana Dawuda, za ka yi manyan abubuwa, ka kuwa yi nasara!” Dawuda dai ya yi tafiyarsa, Saul kuma ya koma gidansa.


Saul ya ce, “Ubangiji ya sa muku albarka, gama kuna jin juyayina.


Shi ne ya ce wa mahaifiyarsa, “Sa'ad da aka sace miki tsabar azurfan nan dubu da ɗari ɗaya (1,100), kin hurta la'ana a kan ɓarayin, na kuwa ji ki. To, ga shi, azurfar na wurina, ni na ɗauka.” Sai mahaifiyarsa ta ce, “Allah ya sa maka albarka, ɗana.”


Ubangiji Allah na Isra'ila, wanda kika zo neman mafaka gare shi, ya sāka miki da cikakken lada saboda abin da kika yi.”


Ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, gama Saul, mahaifina ba zai same ka ba. Za ka zama Sarkin Isra'ila, ni kuma zan zama wazirinka. Saul mahaifina ya san da haka.”


Ubangiji dai zai sāka wa kowa bisa ga adalcinsa da amincinsa. Ubangiji ya bashe ka a hannuna yau, amma na ƙi in kashe wanda Ubangiji ya keɓe.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ