Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 23:26 - Littafi Mai Tsarki

26 Saul yana gefe ɗaya na dutsen, Dawuda kuma da mutanensa suna wancan gefe. Dawuda ya yi sauri ya tsere daga Saul domin Saul da mutanensa suna ƙoƙari su kewaye su, su kama su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 Shawulu yana tafiya a gefe ɗaya na dutsen, Dawuda da mutanensa kuma suna a wancan gefe, suna hanzari su ɓace wa Shawulu. Sa’ad da Shawulu da sojojinsa suka kusa cimma Dawuda da mutanensa don su kama su,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 23:26
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Daga hare-hare na mugaye. Maƙiyana cike da ƙiyayya sun kewaye ni.


Sai kuma su bazu, su mamaye duk duniya, su yi wa sansanin tsarkaka da ƙaunataccen birni ƙawanya, sai wuta ta zubo daga sama ta lashe su.


'Yan'uwa, ba ma so ku jahilta da wahalar da muka sha a ƙasar Asiya, domin kuwa mun ji jiki ƙwarai da gaske, har abin ya fi ƙarfinmu, har ma muka fid da tsammanin rayuwa.


Na ji tsoro, na zaci ka jefar da ni ne daga gabanka. Amma ka ji kukana sa'ad da na yi kira gare ka neman taimako.


Ƙungiyar mugaye na kewaye da ni, Suka taso mini kamar garken karnuka, Suka soke hannuwana da ƙafafuna.


Magabta da yawa sun kewaye ni kamar bijimai, Dukansu suna kewaye da ni, Kamar bijimai masu faɗa na ƙasar Bashan.


Yanzu suna kewaye da ni duk inda na juya, Suna jira su sami dama su fyaɗa ni ƙasa.


Ya Allahnmu, ba za ka hukunta su ba? Ba mu da ƙarfin da za mu yi yaƙi da wannan babban taro da suke zuwa su yi yaƙi da mu. Mun rasa abin da za mu yi, amma a gare ka muke zuba ido.”


Sa'an nan Dawuda ya ce wa fādawansa da suke tare da shi a Urushalima, “Mu tashi mu gudu, in ba haka ba ko ɗayanmu ba zai tsere daga hannun Absalom ba. Sai mu hanzarta mu gudu don kada ya tarar da mu, ya yi mana ɓarna, ya kuma kashe kowa da kowa a birnin.”


Ya ce wa yaron ya yi maza, kada ya tsaya. Sai yaron ya kwashe kiban ya kawo masa.


Sai ta zurarar da Dawuda ta taga, ya gudu, ya tsere.


Aka faɗa wa mutanen Gaza, Samson yana nan. Suka kewaye wurin, suka yi fakonsa a ƙofar garin dukan dare. Suka yi shiru dukan dare, suka ce wa junansu, “Za mu jira sai gari ya waye sa'an nan mu kashe shi.”


Saul da mutanensa suka tafi neman Dawuda. Da Dawuda ya ji labari, sai ya sauka daga dutsen ya zauna a can jejin Mawon. Da Saul ya ji, sai ya bi Dawuda zuwa jejin Mawon.


Suna bin su Dawuda kusa kusa, sai manzo ya zo ya ce wa Saul, “Sai ka komo da sauri domin Filistiyawa sun kawo wa ƙasar hari.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ