Shari'ar shugabannin ƙasar ta cin hanci ce. Firistocinta suna koyarwa don neman riba, Haka kuma annabawa suna annabci don neman kuɗi. Duk da haka suna dogara ga Ubangiji, suna cewa, “Ai, Ubangiji yana tsakiyarmu, Ba masifar da za ta same mu.”
Ku kasa kunne ga abin da Ubangiji yake faɗa, ku da kuke tsoronsa gama ya ce, “Domin kuna da aminci gare ni, waɗansu daga 'yan'uwanku suka ƙi ku, har ba su da hulɗar kome da ku. Suna yi muku ba'a suna cewa, ‘Muna so mu ga kuna murna, saboda haka bari a ɗaukaka Ubangiji.’ Amma su za su sha kunya!
Shi ne ya ce wa mahaifiyarsa, “Sa'ad da aka sace miki tsabar azurfan nan dubu da ɗari ɗaya (1,100), kin hurta la'ana a kan ɓarayin, na kuwa ji ki. To, ga shi, azurfar na wurina, ni na ɗauka.” Sai mahaifiyarsa ta ce, “Allah ya sa maka albarka, ɗana.”
sai ya aiki manzanni da saƙo wurin mutanen Yabesh-gileyad ya ce, “Ubangiji ya sa muku albarka da yake kun yi wa Saul, ubangijinku, wannan alheri, har kuka binne shi.
A lokacin da Allah ya raba ni da gidan mahaifina, ya sa ni yawace yawace, na ce mata, ‘Wannan shi ne alherin da za ki yi mini a duk inda muka je, ki ce da ni ɗan'uwanki ne.’ ”