Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 23:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Sai Dawuda ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ko in tafi in fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi?” Ubangiji kuwa ya ce wa Dawuda, “Tafi, ka yi yaƙi da Filistiyawa, ka ceci mutanen Kaila.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Sai Dawuda ya nemi nufin Ubangiji, ya ce, “In tafi in fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi?” Ubangiji kuwa ya ce masa, “Jeka ka yi yaƙi da Filistiyawa, ka ceci Keyila.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 23:2
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Dawuda kuma ya sāke roƙon Ubangiji. Sai Ubangiji ya amsa masa, ya ce, “Tashi, ka gangara zuwa Kaila, gama zan ba da Filistiyawa a hannunka.”


Dawuda ya kuma roƙi Ubangiji. Ubangiji kuwa ya ce masa, “Kada ka haura zuwa wurinsu gaba da gaba, amma ka bi ta bayansu, ka ɓullo musu daura da itatuwan doka.


Dawuda kuwa ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ko in tafi in yi yaƙi da Filistiyawa? Za ka bashe su a hannuna?” Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka haura, gama hakika, zan ba da Filistiyawa a hannunka.”


“Ya Ubangiji, na sani al'amuran mutum ba a hannunsa suke ba, Ba mutum ne yake kiyaye takawarsa ba


Sai Dawuda ya yi tambaya ga Ubangiji ya ce, “In bi sawun 'yan harin nan? Zan ci musu?” Ya ce masa, “Bi su, gama za ka ci musu, ka ƙwato abin da suka kwashe.”


Lokacin da Abiyata ɗan Ahimelek, ya gudu zuwa wurin Dawuda a Kaila, ya zo da falmaran a hannunsa.


Sai Isra'ilawa suka ɗiba daga cikin guzurin Hiwiyawa, amma ba su nemi shawara wurin Ubangiji ba.


Ubangiji ya ce, “Zan koya maka hanyar da za ka bi, Zan koya maka, in kuma ba ka shawara.


Sai Dawuda ya roƙi Allah, ya ce, “In tafi in yi yaƙi da Filistiyawa? Za ka bashe su a hannuna?” Ubangiji kuwa ya amsa masa, ya ce, “Ka haura, gama zan bashe su a hannunka.”


Bayan da Joshuwa ya rasu, jama'ar Isra'ila suka tambayi Ubangiji suka ce, “Wane ne daga cikinmu zai fara tafiya don ya yaƙi Kan'aniyawa?”


Zai dogara ga Ele'azara, firist, don ya san nufina, ta wurin amfani da Urim da Tummin. Ta haka ne Ele'azara zai bi da Joshuwa da dukan taron jama'ar Isra'ila cikin al'amuransu.”


Suka yi tambaya a wurin Ubangiji, suka ce, “Ko akwai wani dabam?” Ubangiji ya ce, “Ai, ga shi can, ya ɓuya cikin kayayyaki.”


Amma mutanen Dawuda suka ce masa, “Ga shi, nan ma a Yahuza muna jin tsoro, balle mu tafi Kaila mu yi yaƙi da sojojin Filistiyawa.”


Bayan wannan sai Dawuda ya roƙi Ubangiji, ya ce, “Ko in haura in mallaki ɗaya daga cikin garuruwan Yahuza?” Ubangiji ya ce masa, “Ka haura.” Dawuda kuma ya ce, “Zuwa wane gari zan haura?” Sai Ubangiji ya ce masa, “Zuwa Hebron.”


Saul kuwa ya yi tambaya ga Ubangiji, ya ce, “In runtumi Filistiyawa? Za ka bashe su ga Isra'ilawa?” Amma Ubangiji bai amsa masa a wannan rana ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ