Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 23:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Sa'an nan Dawuda da mutanen da suke tare da shi, mutum wajen ɗari shida, suka tashi daga Kaila, suka tafi inda hali ya kai su. Da Saul ya ji Dawuda ya tsere daga Kaila, sai ya fasa tafiya can.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Saboda haka Dawuda da mutanensa wajen mutum ɗari shida suka bar Keyila, suka yi ta tafiya daga wannan wuri zuwa wancan. Sa’ad da aka gaya wa Shawulu cewa Dawuda ya tsere daga Keyila, sai ya fasa tafiya can.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 23:13
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Dawuda ya ce wa mutanensa, “Kowa ya rataya takobinsa.” Ko wannensu kuwa ya rataya takobi. Dawuda kuma ya rataya nasa takobi. Mutum wajen arbaminya suka tafi tare da shi. Mutum metan kuwa suka zauna a wurin kayayyakinsu.


Kowane mutum kuma da yake matse, da wanda ake bi bashi, da wanda ransa ba ya kwance, suka tattaru a wurin Dawuda. Shi kuwa ya zama shugabansu. Sun kai wajen mutum ɗari huɗu.


Jiya jiya ka zo, ba daidai ba ne in sa ka ka yi ta ragaita tare da mu, ga shi, ban san inda zan tafi ba. Koma tare da 'yan'uwanka. Ubangiji ya nuna maka alherinsa, da amincinsa.”


Dukan fādawansa, da matsaransa, wato dukan Keretiyawa, da dukan Feletiyawa, da dukan Gittiyawa, sojoji ɗari shida waɗanda suka bi Dawuda tun daga Gat suka wuce a gabansa.


Yakan birkitar da shirye-shiryen masu wayo.


Waɗanda ake zalunta suka dube shi suka yi murna, Ba za su ƙara ɓacin rai ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ