Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 22:7 - Littafi Mai Tsarki

7-8 Sai ya ce wa fādawan da suke tsaye kewaye da shi, “Ku ji, ya ku mutanen Biliyaminu, ɗan Yesse zai ba kowannenku gonaki, da gonakin inabi ne? Zai maishe ku shugabanni na dubu dubu, da na ɗari ɗari, har da dukanku kuka yi mini maƙarƙashiya? Ba wanda ya sanar da ni sa'ad da ɗana ya haɗa kai da ɗan Yesse? Ba wanda ya damu saboda da ni, balle a faɗa mini yadda ɗana ya kuta barana ya tayar mini, yana fakona, kamar yadda yake a yau?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Ya ce musu, “Mutanen Benyamin, ku saurara; ɗan Yesse zai iya ba dukanku filaye da gonakin inabi ne? Zai ba dukanku shugabanci na dubbai ko shugabanci na ɗari-ɗari?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 22:7
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da mutanen Isra'ila suka ga sarki ya ƙi jin roƙonsu, sai suka yi ihu, suna cewa, “A yi ƙasa da Dawuda da iyalinsa. Me suka taɓa yi mana? Mazajen Isra'ila, bari duka mu tafi gida! Mu bar Rehobowam ya lura da kansa!” Jama'ar Isra'ila fa suka tayar,


Rana tana zuwa sa'ad da sabon sarki zai fito daga cikin gidan sarautar Dawuda, zai zama alama ga sauran al'umma. Za su tattaru a birnin sarautarsa su girmama shi.


Gidan sarautar Dawuda kamar itacen da aka sare ne, amma kamar yadda rassa sukan toho daga cikin kututture, haka nan za a sami sabon sarki daga zuriyar Dawuda.


Da can akwai wani mutumin banza, ana ce da shi Sheba, ɗan Bikri, daga kabilar Biliyaminu. Shi kuwa ya busa ƙaho, ya ce, “Ba mu da rabo a wurin Dawuda, ba mu kuwa da gado wurin ɗan Yesse. Ya Isra'ilawa, kowa ya gudu zuwa alfarwarsa.”


Nabal ya amsa wa barorin Dawuda, ya ce, “Wane ne Dawuda? Wane ne ɗan Yesse? A kwanakin nan akwai barori da yawa waɗanda suka tayar wa iyayengijinsu.


Saul ya ce masa, “Me ya sa ka yi mini maƙarƙashiya, kai da ɗan Yesse, da yake ka ba shi abinci, da takobi, ka kuma roƙar masa Allah, ga shi yanzu, ya tayar mini, yana fakona, kamar yadda yake yi a yau?”


Sa'an nan Doyeg, mutumin Edom, da yake tsaye tare da fādawan Saul, ya ce, “Na ga ɗan Yesse yana zuwa Nob wurin Ahimelek, ɗan Ahitub.


Sai Saul ya husata da Jonatan, ya ce masa, “Kai yaron banza ne, mai ƙin ji, ai, na sani kana goyon bayan ɗan Yesse don ka wulakantar da kanka da mahaifiyarka.


Amma kashegari, wato rana ta biyu ta amaryar watan, ba kowa kuma wurin zaman Dawuda, sai Saul ya ce wa Jonatan, ɗansa, “Me ya sa ɗan Yesse bai zo wurin cin abinci ba, jiya da yau?”


Dawuda kuwa ya yi ta yin nasara cikin ayyukansa duka, domin Ubangiji yana tare da shi.


Dawuda kuwa ya shirya sojojin da suke tare da shi, sa'an nan ya naɗa musu shugabanni na dubu dubu da na ɗari ɗari.


Sa'an nan waɗansu daga cikin mazajen Biliyaminu da na Yahuza, suka zo wurin Dawuda a kagararsa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ