Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 22:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Sai Saul ya ji labari an gane inda Dawuda da mutanensa suke. Saul kuwa yana zaune a Gibeya a gindin itacen tsamiya a kan tudu, yana riƙe da mashinsa. Dukan fādawansa suna tsaye kewaye da shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Sai Shawulu ya sami labari cewa an ga Dawuda da mutanensa. Shawulu kuwa yana zaune da māshinsa kusa a ƙarƙashin itacen tsamiya a tudun Gibeya, tare da dukan ma’aikatansa kewaye da shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 22:6
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Saul ya jefe shi da mashi don ya kashe shi. Sai Jonatan ya gane lalle mahaifinsa ya yi niyya ya kashe Dawuda.


Ubangiji kuma ya sa mugun ruhu ya sauko kan Saul sa'ad da yake zaune a gidansa, da mashi a hannunsa. Dawuda kuma yana ta kaɗa masa garaya.


Kashegari Allah ya sa mugun ruhu ya sauka a kan Saul, sai ya yi ta maganganu a gidansa kamar mahaukaci, sai Dawuda ya yi ta kaɗa masa garaya kamar yadda ya saba yi. Saul kuwa yana riƙe da mashi.


Ta zauna a gindin giginyar Debora tsakanin Rama da Betel, a ƙasar tudu ta Ifraimu. Isra'ilawa sukan haura zuwa wurinta don ta yi musu shari'a.


Ibrahim kuma ya dasa itacen tsamiya a Biyer-sheba, a can ya yi kira bisa sunan Ubangiji, Allah Madawwami.


Saul kuwa yana zaune a karkarar Gibeya a gindin itacen rumman a Migron. Mutum wajen ɗari shida suna tare da shi.


Suka binne ƙasusuwansu a gindin itacen tsamiya a Yabesh, sa'an nan suka yi azumi kwana bakwai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ