Dawuda kuwa ya ce wa Abiyata, “A ran nan Doyeg, mutumin Edom, yana wurin, na sani lalle zai faɗa wa Saul. Ni na zama sanadin mutuwar dukan mutanen gidan mahaifinka.
Zan dai bar ɗaya daga zuriyarka da rai, zai yi mini aikin firist, amma zai makance ya fid da zuciya ga kome. Dukan sauran zuriyarka kuwa za su yi mutuwa ƙarfi da yaji.