1 Samaʼila 22:17 - Littafi Mai Tsarki17 Ya ce wa matsara da suke tsaye kewaye da shi, “Ku fāɗa wa firistocin Ubangiji, ku kashe su gama suna goyon bayan Dawuda, ga shi, sun sani ya gudu, amma ba su faɗa mini ba.” Amma barorin sarki ba su yarda su fāɗa wa firistocin Ubangiji ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202017 Sai sarki ya umarci matsaran da suke tsaye kusa da shi ya ce, “Ku kakkashe firistocin Ubangiji, gama su ma sun goyi bayan Dawuda. Sun san yana gudu, duk da haka ba su gaya mini ba.” Amma ma’aikatan sarki ba su yarda su sa hannu su kashe firistocin Ubangiji ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Amma jama'a suka ce wa Saul, “Jonatan da ya yiwo babbar nasara domin Isra'ila, a ce za a kashe shi? Kai, a'a! Mun yi alkawari ga Ubangiji mai rai, Jonatan ba zai yi hasarar ko gashi guda daga kansa ba. Abin da ya yi a yau, da taimakon Allah ne ya yi.” Da haka mutane suka ceci Jonatan, har ba a kashe shi ba.