Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 22:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Shi kuwa ya roƙi Ubangiji domin Dawuda, ya kuma ba shi guzuri, har ya ba shi takobin Goliyat, Bafilisten.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Ahimelek ya roƙi Ubangiji saboda shi, ya kuma ba shi guzuri da takobin Goliyat Bafilistin.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 22:10
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Zai dogara ga Ele'azara, firist, don ya san nufina, ta wurin amfani da Urim da Tummin. Ta haka ne Ele'azara zai bi da Joshuwa da dukan taron jama'ar Isra'ila cikin al'amuransu.”


Sai Dawuda ya yi tambaya ga Ubangiji ya ce, “In bi sawun 'yan harin nan? Zan ci musu?” Ya ce masa, “Bi su, gama za ka ci musu, ka ƙwato abin da suka kwashe.”


Dawuda kuma ya sāke roƙon Ubangiji. Sai Ubangiji ya amsa masa, ya ce, “Tashi, ka gangara zuwa Kaila, gama zan ba da Filistiyawa a hannunka.”


Sai Dawuda ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ko in tafi in fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi?” Ubangiji kuwa ya ce wa Dawuda, “Tafi, ka yi yaƙi da Filistiyawa, ka ceci mutanen Kaila.”


Dawuda kuma ya ce, “Mutanen Kaila za su bashe ni da mutanena a hannun Saul?” Ubangiji ya ce masa, “Za su bashe ku.”


Yau ne na fara roƙar masa Allah? A'a, kada dai sarki ya zargi baransa ko gidan mahaifina duka, gama baranka bai san kome a kan wannan ba.”


Saul ya ce masa, “Me ya sa ka yi mini maƙarƙashiya, kai da ɗan Yesse, da yake ka ba shi abinci, da takobi, ka kuma roƙar masa Allah, ga shi yanzu, ya tayar mini, yana fakona, kamar yadda yake yi a yau?”


Suka yi tambaya a wurin Ubangiji, suka ce, “Ko akwai wani dabam?” Ubangiji ya ce, “Ai, ga shi can, ya ɓuya cikin kayayyaki.”


Sarki kuwa ya aika a kira Ahimelek, firist, ɗan Ahitub, da dukan mutanen gidan mahaifinsa, da firistocin da suke a Nob. Dukansu kuwa suka zo wurin sarki.


Sai Dawuda ya tashi, yana gudu ke nan daga wurin Saul. Ya tafi wurin Akish, Sarkin Gat.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ