1 Samaʼila 21:9 - Littafi Mai Tsarki9 Firist ya ce, “Ga takobin Goliyat, Bafiliste wanda ka kashe a kwarin Ila, a naɗe da zane a bayan falmaran. Idan kana so ka ɗauka, sai ka ɗauka, gama banda shi, ba wani takobi a nan.” Dawuda kuwa ya ce, “Ai, ba wanda ya fi wannan, sai ka ba ni shi.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 Sai firist ya ce, “Takobin Goliyat Bafilistin nan wanda ka kashe a Kwarin Ela yana nan. An naɗe shi da ƙyallen aka ajiye a bayan Efod, in kana so, sai ka ɗauka. Ba wani takobi kuma sai wancan.” Dawuda ya ce, “Ba ni shi, ai, ba wani kamar sa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |