40 Sa'an nan Jonatan ya ba yaron makamansa, ya ce masa, “Kai su gari.”
40 Yonatan ya ba wa yaron makaman ya ce, “Ka ɗauka ka koma gari.”
Amma yaron bai san abin da ake nufi ba. Jonatan da Dawuda kaɗai suka san abin da ake ciki.
Da yaron ya tafi, sai Dawuda ya tashi daga inda ya ɓuya kusa da tarin duwatsun, ya rusuna har sau uku. Sa'an nan suka sumbaci juna, suka yi kuka, amma Dawuda ya fi yi.