Ya yi kasai da ransa har ya kashe Bafilisten, Ubangiji kuwa ya ba Isra'ilawa babbar nasara. Kai ma ka gani, ka kuwa yi murna. Me ya sa za ka ɗauki alhakin Dawuda, wanda bai yi maka laifin kome ba?”
Ya sāke faɗa musu, a faɗa ta uku, “Ta wane hali? Wane mugun abu ya yi? Ai, ban sami dalilin kisa a gare shi ba. Saboda haka, zan yi masa bulala in sake shi.”
Duk makomarsu ɗaya ce, wannan ita ce ɓarnar da take faruwa a duniya. Muddin mutane suna da rai tunaninsu cike yake da mugunta da rashin hankali. Bayan haka sukan mutu.
Jonatan kuwa ya yabi Dawuda a gaban Saul, ya ce masa, “Kada sarki ya yi wa baransa, Dawuda, laifi, gama shi bai yi maka laifi ba, ayyukansa kuma a gare ka masu kyau ne.
Ahimelek kuwa ya ce wa sarki, “Daga cikin barorinka duka wa yake da aminci kamar Dawuda? Wane ne surukin sarki? Wane ne shugaban jarumawanka, wanda ake girmamawa a gidanka?
Sa'an nan Dawuda ya gudu daga Nayot ta Rama, ya zo wurin Jonatan, ya ce masa, “Me na yi? Mene ne laifin da na yi wa mahaifinka da yake so ya kashe ne?”