Idan mahaifinka bai gan ni ba, sai ka ce masa, ni na roƙe ka ka bar ni in gaggauta zuwa Baitalami, garinmu, domin akwai ba da sadaka ta shekara saboda dukan gidanmu.
Amma kashegari, wato rana ta biyu ta amaryar watan, ba kowa kuma wurin zaman Dawuda, sai Saul ya ce wa Jonatan, ɗansa, “Me ya sa ɗan Yesse bai zo wurin cin abinci ba, jiya da yau?”
Ya ce mini, ‘In ka yarda ka bar ni in tafi, gama a gidanmu ana ba da sadaka a gari, ɗan'uwana kuwa ya umarce ni in je. Idan na sami tagomashi a wurinka ka bar ni in tafi in ga 'yan'uwana.’ Abin da ya sa bai zo ba ke nan.”