Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 20:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Zan aiki yaro ya tafi ya nemo kiban. Idan na ce masa, ‘Duba, ga kiban kusa da kai, ka kawo su,’ To, sai ka fito, ka zo, wato lalle kome lafiya ke nan, ba abin da zai cuce ka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Sa’an nan zan aiki yaro in ce masa, ‘Je ka nemo kibiyoyin.’ In na ce masa, ‘Duba, kibiyoyin suna wannan gefen da kake, kawo su,’ sai ka fito, wato, tabbatacce muddin Ubangiji yana raye, ka tsira, ba wani hatsari.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 20:21
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Waɗanda suka yi rantsuwa da gumakan Samariya, Waɗanda suka ce, ‘Na rantse da gunkin Dan, Da ran gunkin Biyer-sheba,’ Irin waɗannan mutane za su fāɗi, Ba za su ƙara tashi ba.”


Zai zama kuwa, idan za su himmantu su koyi al'amuran jama'ata, su yi rantsuwa da sunana, su ce, ‘Da zatin Ubangiji,’ kamar yadda suka koya wa jama'ata yin rantsuwa da Ba'al, sa'an nan za a gina su a tsakiyar jama'ata.


Ko da yake suna cewa, ‘Na rantse da ran Ubangiji,’ Duk da haka rantsuwar ƙarya suke yi.”


Idan kun yi rantsuwa kuka ce, ‘Har da ran Ubangiji kuwa,’ Da gaskiya, da aminci, da adalci, Sa'an nan sauran al'umma za su so in sa musu albarka, Za su kuma yabe ni.”


Zan harba kibau guda uku kusa da tarin duwatsun, kamar ina harbin wani abu ne.


Amma idan na ce wa yaron, ‘Duba, kiban suna a gabanka,’ To, ka tafi, gama Ubangiji ya sallame ka, ka tafi.


Sai ya ce wa yaron, “Yi gudu, ka nemo kiban da zan harba.” Sa'ad da yaron ya ruga, sai ya harba kibiya gaba da shi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ