20 Zan harba kibau guda uku kusa da tarin duwatsun, kamar ina harbin wani abu ne.
20 Zan harbi kibiya uku ta wajen, sai ka ce dai ina harbin baka.
A rana ta uku za a gane ba ka nan sosai, to, sai ka tafi, ka ɓuya a wurin da ka ɓuya a waccan rana. Ka zauna kusa da tarin duwatsu.
Zan aiki yaro ya tafi ya nemo kiban. Idan na ce masa, ‘Duba, ga kiban kusa da kai, ka kawo su,’ To, sai ka fito, ka zo, wato lalle kome lafiya ke nan, ba abin da zai cuce ka.
Sai ya ce wa yaron, “Yi gudu, ka nemo kiban da zan harba.” Sa'ad da yaron ya ruga, sai ya harba kibiya gaba da shi.