Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 20:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Jonatan ya ce masa, “Allah ya sawwaƙa, ba za a kashe ka ba, gama babana yakan faɗa mini kome, ƙarami ko babba, kafin ya aikata. To, me zai sa babana ya ɓoye mini wannan? Wannan ba haka yake ba.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Yonatan ya ce, “Faufau, ba za ka mutu ba! Ka ji nan, mahaifina ba ya yin kome ba tare da ya shawarce da ni ba. Me ya sa ya ɓoye mini wannan? Ba zai yiwu ba.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 20:2
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Domin kuwa maganar da ka faɗa mini na faɗa musu, sun kuwa karɓa, sun kuma san hakika na fito daga wurinka ne, sun kuma gaskata kai ne ka aiko ni.


Ana gobe Saul zai tafi wurin Sama'ila, Ubangiji ya bayyana wa Sama'ila.


Sa'an nan Jonatan ya ce wa Dawuda, “Ubangiji Allah na Isra'ila zai zama shaida. Gobe war haka, ko jibi zan tattauna maganar da mahaifina, idan da nufin alheri zuwa gare ka, zan aika, in faɗa maka.


Amma jama'a suka ce wa Saul, “Jonatan da ya yiwo babbar nasara domin Isra'ila, a ce za a kashe shi? Kai, a'a! Mun yi alkawari ga Ubangiji mai rai, Jonatan ba zai yi hasarar ko gashi guda daga kansa ba. Abin da ya yi a yau, da taimakon Allah ne ya yi.” Da haka mutane suka ceci Jonatan, har ba a kashe shi ba.


Allah ya sawwaƙa mana mu tayar wa Ubangiji, mu bar bin Ubangiji, har mu gina wani bagade don miƙa hadayu na ƙonawa, da na gari, da na sadaka, banda bagaden Ubangiji Allahnmu, wanda yake a gaban mazauninsa.”


Suka ce masa, “Don me shugabana zai faɗi irin waɗannan maganganu? Allah ya sawwaƙe da bayinka za su aikata irin wannan!


Nan gaba ba sauran in ce da ku bayi, don bawa bai san abin da ubangijinsa yake yi ba. Sai dai in ce da ku aminai, domin na sanar da ku duk abin da na jiyo wurin Ubana.


Sai ya zo ya hallaka manoman nan, ya ba waɗansu garkar.” Da suka ji haka, suka ce, “Allah ya sawwaƙe!”


Ubangiji ya ba ni fahimi, Ban kuwa yi masa tayarwa ba Ko in juya in rabu da shi.


Ba ka bukatar baye-baye da hadayu, Ba ka so a miƙa maka hadayun ƙonawa Na dabbobi a bisa bagade ba, Ko baya-baye don a kawar da zunubai. A maimakon haka, ka ba ni kunnuwan da zan saurare ka.


Jama'a kuwa suka amsa suka ce, “Allah ya kiyashe mu da rabuwa da Ubangiji, har a ce mu bauta wa gumaka.


Sa'an nan Dawuda ya gudu daga Nayot ta Rama, ya zo wurin Jonatan, ya ce masa, “Me na yi? Mene ne laifin da na yi wa mahaifinka da yake so ya kashe ne?”


Amma Dawuda ya rantse masa, ya ce, “Mahaifinka ya hakikance na sami tagomashi a wurinka, domin haka ba zai sanar maka da wannan ba, don kada ya baƙanta maka rai. Na rantse da Ubangiji da kai kuma, mataki ɗaya yake tsakanina da mutuwa!”


Abokin ɓarawo mugun maƙiyin kansa ne, yana jinsa yana ta rantsuwa, amma ba zai ce kome ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ