11 Jonatan kuwa ya ce masa, “Zo mu tafi saura.” Sai su biyu suka tafi saura.
11 Yonatan ya ce, “Zo mu fita zuwa fili.” Sai suka tafi tare.
Sa'an nan Dawuda ya ce wa Jonatan, “Wane ne zai faɗa mini idan mahaifinka ya amsa maka da fushi?”
Sa'an nan Jonatan ya ce wa Dawuda, “Ubangiji Allah na Isra'ila zai zama shaida. Gobe war haka, ko jibi zan tattauna maganar da mahaifina, idan da nufin alheri zuwa gare ka, zan aika, in faɗa maka.