Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 2:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Ubangiji ne yake kashewa, ya kuma rayar, Yana kai mutane kabari, Ya kuma tā da su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 “Ubangiji ne ke kawo mutuwa, yă kuma rayar yana kai ga kabari, yă kuma tā da.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 2:6
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“ ‘Ku duba fa, ni ne shi, Ba wani Allah, banda ni, Nakan kashe, in rayar, Nakan sa rauni, nakan kuma warkar, Ba wanda zai cece su daga hannuna.


Mutanenmu da suka mutu za su sāke rayuwa! Jikunansu za su sāke rayuwa! Dukan waɗanda suke kwance cikin kaburburansu Za su farka, su yi waƙa don farin ciki! Kamar laimar raɓa wanda yake wartsakar da duniya, Haka Ubangiji zai rayar da waɗanda suka daɗe da mutuwa.


Da Sarkin Isra'ila ya karanta takardar, sai ya keta tufafinsa, ya ce, “Ni Allah ne, da zan kashe in rayar, har mutumin nan zai aiko mini da cewa in warkar da mutum daga kuturtarsa? Ku duba fa, ku ga yadda yake nemana da faɗa.”


ni ne kuma Rayayye. Dā na mutu, amma ga shi a yanzu, ina a raye har abada abadin, ina kuwa da mabuɗan mutuwa da na Hades.


Allah yakan yi maganin raunin da ya yi maka, Ciwon da ya ji maka da hannunsa, Da hannunsa yakan warkar.


Yesu ya ce mata, “Ai, ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai. Wanda ya gaskata da ni, ko ya mutu zai rayu.


Wato, kamar yadda Yunusa ya yi kwana uku dare da rana cikin wani babban kifi, haka kuma Ɗan Mutum zai yi kwana uku dare da rana a cikin ƙasa.


Mutuwa ta ɗaure ni da igiyarta tam, Razanar kabari ta auka mini, Na cika da tsoro da alhini.


Amma Dawuda ya rantse masa, ya ce, “Mahaifinka ya hakikance na sami tagomashi a wurinka, domin haka ba zai sanar maka da wannan ba, don kada ya baƙanta maka rai. Na rantse da Ubangiji da kai kuma, mataki ɗaya yake tsakanina da mutuwa!”


Allahnmu, Allah Mai Ceto ne, Shi ne Ubangiji, Ubangijinmu, Wanda yake cetonmu daga mutuwa.


Da lokacin kisa, da lokacin rayarwa, Da lokacin rushewa, da lokacin ginawa.


Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, waɗannan ƙasusuwa kuwa za su rayu?” Ni kuwa na amsa na ce, “Ya Ubangiji Allah, sani na gare ka.”


“Domin haka ka yi annabci ka ce musu, ni Ubangiji Allah na ce zan buɗe kaburburansu, in tashe su daga cikin kaburburansu. Zan kuma komar da su gida zuwa ƙasar Isra'ila.


Ubangiji kuwa ya amsa wa Iliya, ran yaron ya komo cikinsa, sai ya farfaɗo.


Ku raira yabo ga Ubangiji, Ku amintattun jama'arsa! Ku tuna da abin da Mai Tsarki ya aikata, Ku yi masa godiya!


Ka aiko mini da wahala da azaba, Amma za ka mayar mini da ƙarfina, Za ka tashe ni daga kabari.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ