Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 2:29 - Littafi Mai Tsarki

29 Me ya sa kuke haɗama a kan hadayuna da sadakokin da na umarta? Eli, don me kake girmama 'ya'yanka fiye da ni, ka bar su suna ta cinye rabo mafi kyau na hadayun jama'ata Isra'ila?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

29 Don me kuke rena hadayata da sadakokina da na ƙayyade domin mazaunina? Don me kake girmama ’ya’yanka fiye da ni ta wurin cinye sashe mafi kyau na kowane hadayar da mutanena Isra’ila suka miƙa?’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 2:29
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Wanda duk ya fi son ubansa ko uwarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma ya fi son ɗansa ko 'yarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba.


“Yeshurun ya yi ƙiba, yana harbin iska, Ka yi ƙiba, ka yi kauri, ka yi sumul. Ya rabu da Allahn da ya yi shi, Ya raina Dutsen Cetonsa.


“Duk mai zuwa wurina, in bai fi ƙaunata da ubansa, da uwa tasa, da mata tasa, da 'ya'yansa, da 'yan'uwansa mata da maza, har ma ransa ba, ba zai iya zama almajirina ba.


Amma hikimar nan ta Sama, da farko dai tsattsarka ce, mai lumana ce, saliha ce, mai sauƙin kai, mai tsananin jinƙai, mai yawan alheri, mai kaifi ɗaya, sahihiya kuma.


Suka aiko almajiransu wurinsa tare da waɗansu mutanen Hirudus, suka ce, “Malam, ai, mun sani kai mai gaskiya ne, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi, ba ka kuma zaɓen kowa, don ka ɗauki kowa da kowa daidai.


Ga abin da Ubangiji ya ce a kan annabawan da suka bi da mutanensa a karkace, Waɗanda suke cewa, “Salama,” sa'ad da suke da abinci, Amma sukan kai yaƙin shahada Ga wanda bai ba su abin sawa a baka ba.


Suna ciyar da kansu da zunubin mutanena, Suna haɗamar ribar muguntarsu.


“Ɗan mutum, ka yi annabci a kan makiyayan Isra'ila, ka ce musu, ‘Ku masu kiwon mutanen Isra'ila, ni Ubangiji Allah na ce, kaito, kaito, ku masu kiwon mutanen Isra'ila, kuna kiwon kanku kawai! Ashe, ba makiyaya ne suke kiwon tumaki ba?


Da jama'ar Isra'ila suka ci ƙasar, sai suka tattaru a Shilo inda suka kafa alfarwa ta sujada.


Wanda ya ce wa mahaifinsa da mahaifiyarsa, ‘Ban kula da ku ba.’ Ya ce wa 'yan'uwansa su ba nasa ba ne. Ya kuma ƙyale 'ya'yansa, Domin sun kiyaye maganarka, Sun riƙe alkawarinka.


“Ku yi gaskiya da adalci cikin shari'a, kada ku ma ku yi wa matalauci son zuciya, ko ku goyi bayan mawadaci.


Saboda haka, a nan gaba ba mā ƙara duban kowane mutum bisa ga ɗabi'ar jiki kawai, domin ko da yake mun taɓa duban Almasihu bisa ga ɗabi'ar jiki, yanzu ba ma ƙara dubansa haka.


Ai, irin waɗannan mutane ba sa bauta wa Ubangijinmu Almasihu, sai dai cikinsu. Ta romon kunne da daɗin baki suke yaudarar masu sauƙin kai.


Kun saɓi sunana a cikin mutanena don a tafa muku sha'ir, a ba ku ɗan abinci. Kuna kashe mutane waɗanda bai kamata su mutu ba, kuna barin waɗanda bai kamata su rayu ba ta wurin ƙaryace-karyacen da kuke yi wa mutanena waɗanda suke kasa kunne ga ƙaryace-ƙaryacen.’


Na fāɗa masa zan hukunta gidansa har abada saboda 'ya'yansa sun faɗi mugayen maganganu a kaina. Eli kuwa ya sani, amma bai kwaɓe su ba.


Ya Ubangiji, ina ƙaunar Haikali inda zatinka yake, Inda ɗaukakarka yake zaune.


Ga shi, ina gāba da ku, zan nemi tumakina a hannunku. Zan hana ku yin kiwon tumakin, ku kuma ba za ku ƙara yin kiwon kanku ba. Zan ƙwace tumakina daga hannunku, domin kada su ƙara zama abincinku.’ ”


Amma har a shekara ta ashirin da uku ta sarautar sarki Yowash, firistocin ba su yi wani gyara a Haikalin ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ