Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 2:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Sai ya caka rinon a cikin tukunyar, to, duk abin da ya cako wannan ya zama na firist. Haka suka yi ta yi wa dukan Isra'ilawa da suka zo miƙa hadaya a Shilo.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 zai soka cokali mai yatsun a tukunyar, ko butar da ake dafan naman. Duk abin da cokali mai yatsun ya cako daga tukunyar, ya zama na firist. Haka aka yi ta yi wa Isra’ilawan da suka zo miƙa hadaya a Shilo.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 2:14
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Suna kama da karnuka masu zarin ci, ba su taɓa samun abin da ya ishe su ba. Makiyayan nan kuma ba haziƙai ba ne, dukansu, kowa ya nufi inda ya ga dama. Kowa yana ta nemar wa kansa riba.


Me ya sa kuke haɗama a kan hadayuna da sadakokin da na umarta? Eli, don me kake girmama 'ya'yanka fiye da ni, ka bar su suna ta cinye rabo mafi kyau na hadayun jama'ata Isra'ila?


Gama Ubangiji ya ba Haruna da 'ya'yansa maza, ƙirjin da aka kaɗa da cinyar da aka ɗaga, su zama rabonsu daga cikin hadayu na salama na Isra'ilawa. Ya ba Haruna, firist, da 'ya'yansa maza, su zama rabonsu har abada daga cikin hadayu na Isra'ilawa.


“Da ma wani daga cikinku ya rufe ƙofofin Haikali don kada ku shiga, ku hura wuta marar amfani a bisa bagadena! Ban ji daɗinku ba. Ba zan karɓi hadayun da kuke kawo mini ba,” in ji Ubangiji Mai Runduna.


Ko ka'idodi game da abin da firistoci za su karɓa a hannun jama'a. A maimakon haka, lokacin da mutum ya je domin ya miƙa hadayarsa, sai baran firist ya zo da rino a hannunsa a sa'ad da ake dafa naman.


Tun kuma kafin a ƙona kitse, baran firist ɗin yakan zo ya ce wa wanda yake yin hadayar. “Ka ba ni wanda firist zai gasa, gama ba zai karɓi dafaffen nama daga gare ka ba, sai dai ɗanye.”


Kuna cin naman mutanena, kuna feɗe fatar jikinsu, Kuna kakkarya ƙasusuwansu, Kuna yanyanka su gunduwa gunduwa kamar naman da za a sa a tukunya.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ