19 Aka faɗa wa Saul cewa, “Dawuda yana a Nayot ta Rama.”
19 Shawulu ya sami labari cewa, “Dawuda yana Nayiwot a Rama.”
Idan mai mulki yana kasa kunne ga maganganun ƙarya, dukan ma'aikatansa za su zama maƙaryata.
Zifawa suka zo wurin Saul a Gibeya suka ce, “Ba ga Dawuda yana ɓuya a kan tudun Hakila wanda yake gaban Yeshimon ba?”
Sai Zifawa suka haura zuwa wurin Saul a Gibeya, suka ce masa, “Dawuda ya ɓuya a ƙasarmu cikin Horesh a kan tudun Hakila da yake kudu da jejin Yahuza.
Dawuda ya gudu, ya tsere zuwa wurin Sama'ila a Rama, ya faɗa masa dukan abin da Saul ya yi masa. Shi da Sama'ila suka tafi suka zauna a Nayot.
Sai ya aika da manzanni su tafi su kama Dawuda. Da suka kai, suka iske ƙungiyar annabawa suna annabci, Sama'ila kuwa yana tsaye a gabansu. Ruhun Allah ya sauko a kan manzannin Saul, su kuma suka yi annabci.