Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 19:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Saul kuwa ya yi shiri ya nashi Dawuda, ya kafe shi ga bango. Da ya nashe shi, sai ya goce, mashin ya sami bangon. Dawuda kuwa ya gudu, ya tsere.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Shawulu ya yi ƙoƙari yă kafe shi da bango da māshinsa, amma Dawuda ya goce sa’ad da Shawulu jefa māshin a bango. A daren nan Dawuda ya nemi hanya ya gudu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 19:10
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Saul ya jefe shi da mashi don ya kashe shi. Sai Jonatan ya gane lalle mahaifinsa ya yi niyya ya kashe Dawuda.


Yana cewa a ransa, “Zan nashe shi in kafe shi da bango.” Sau biyu yana cakar Dawuda da mashi, amma Dawuda ya goce.


Hikima, da haziƙanci, da basira, ba kome suke ba gāba da Ubangiji.


Sai suka sāke ƙoƙarin kama shi, amma ya fita daga hannunsu.


Amma ya ratsa ta tsakiyarsu, ya yi tafiyarsa.


In sun tsananta muku a wannan gari, ku gudu zuwa na gaba. Gaskiya, ina gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan garuruwan Isra'ila, Ɗan Mutum zai zo.


Ubangiji ya ce, “Me zan yi da ke, ya Ifraimu? Me zan yi da ke, ya Yahuza? Ƙaunarku tana kama da ƙāsashi, Kamar kuma raɓar da take watsewa da wuri.


Amma ba makamin da aka ƙera da ya isa ya cuce ki, Za ki iya amsa wa dukan waɗanda za su yi ƙararki. Zan kāre bayina, In kuwa ba su nasara.” Ubangiji ne ya faɗa.


Mun kuɓuta kamar tsuntsu daga tarkon mai farauta, Tarkon ya tsinke, mun 'yantu!


Mutumin kirki yakan sha wahala da yawa, Amma Ubangiji yakan cece shi daga cikinsu duka.


Ya cece ni daga magabtana masu ƙarfi, Daga kuma dukan masu ƙina, Gama sun fi ƙarfina!


Saul kuwa ya saurari maganar Jonatan, ya rantse masa ya ce, “Hakika, ba za a kashe shi ba.”


suka i, wa ikon wuta, suka tsere wa kaifin takobi, suna marasa ƙarfi sai suka zama masu ƙarfi, suka yi jaruntaka a wajen yaƙi, suka fatattaka rundunar waɗansu ƙasashe.


Ba su kasalar aikata mugunta, kullum a shirye suke su yi kisankai.


Kashegari Allah ya sa mugun ruhu ya sauka a kan Saul, sai ya yi ta maganganu a gidansa kamar mahaukaci, sai Dawuda ya yi ta kaɗa masa garaya kamar yadda ya saba yi. Saul kuwa yana riƙe da mashi.


Mugu yakan yi fakon mutumin kirki, Yă yi ƙoƙari yă kashe shi,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ