9 Tun daga wannan rana Saul ya fara kishin Dawuda.
9 Tun daga wannan lokaci zuwa gaba, Shawulu ya dinga kishin Dawuda.
kada kuma ku bar wa Iblis wata ƙofa.
da kwaɗayi, da mugunta, da ha'inci, da fajirci, da kishi, da yanke, da girmankai, da kuma wauta.
Ashe, ba ni da ikon yin abin da na ga dama da abin da yake mallakata? Ko kuwa kana jin haushin alherina ne?’
Yakubu kuma ya ga ba shi da farin jini a wurin Laban kamar dā.
'Yan'uwa, kada ku yi wa juna gunaguni, don kada a hukunta ku. Ga mai shari'a a bakin ƙofa!
Wannan waƙa ta ba Saul haushi, ya ce, “Sun ba Dawuda dubun dubbai, amma dubbai kawai suka ba ni, me kuma ya rage masa, ai, sai sarauta.”
Kashegari Allah ya sa mugun ruhu ya sauka a kan Saul, sai ya yi ta maganganu a gidansa kamar mahaukaci, sai Dawuda ya yi ta kaɗa masa garaya kamar yadda ya saba yi. Saul kuwa yana riƙe da mashi.
Sai Saul ya yi magana da Jonatan, ɗansa, da dukan fādawansa, cewa yana shiri ya kashe Dawuda. Amma Jonatan ɗan Saul yana jin daɗin Dawuda ƙwarai.
Fushi mugun abu ne mai hallakarwa, amma duk da haka bai kai ga kishi ba.
Na gane dalilin da ya sa mutane suke aiki ƙwarai don su ci nasara, so suke su fi kowa samu. Wannan ma aikin banza ne harbin iska kawai.