Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 18:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Ya yi tunani a ransa ya ce, “Zan ba shi ita don ta zamar masa sanadin da zai mutu ta hannun Filistiyawa.” Don haka sai Saul ya ce wa Dawuda a karo na biyu, “Yanzu dai za ka zama surukina.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 “Zan ba shi ita tă zama masa tarko, da haka Filistiyawa za su same shi.” Shawulu ya ce wa Dawuda, “Yanzu kana da dama sau na biyu ka zama surukina.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 18:21
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Saul ya ce wa Dawuda, “Ga Merab babbar 'yata, zan ba ka ita ka aura, idan ka yi mini aikin jaruntaka, wato ka yi yaƙin Ubangiji.” (Gama Saul yana tsammani ta wannan hanya Filistiyawa za su kashe Dawuda, ba lalle sai shi da kansa ya kashe shi ba.)


Harshensu kibiya ce mai dafi, yana faɗar ƙarya, Kowa yana maganar alheri da maƙwabcinsa Amma a zuciyarsa yana shirya masa maƙarƙashiya.


Da fādawan suka faɗa wa Dawuda abin da Saul ya ce, sai Dawuda ya ji daɗi ƙwarai ya zama surukin sarki. Kafin lokacin da aka yanka masa ya yi, sai Dawuda ya tashi, ya tafi tare da mutanensa, suka kashe Filistiyawa ɗari biyu. Ya kawo loɓarsu duka, aka ba sarki, domin ya zama surukin sarki. Saul kuwa ya aurar da Mikal, 'yarsa, ga Dawuda.


Fādawan Fir'auna kuwa suka ce masa, “Har yaushe mutumin nan zai riƙa jawo mana masifa? Ka saki mutanen, su fita su yi wa Ubangiji Allahnsu sujada. Ashe, har yanzu ba ka sani Masar ta lalace ba?”


“Gama an sami mugaye, a cikin jama'ata, Suna kwanto kamar masu kafa ashibta. Sun ɗana tarko su kama mutane.


Mutum wanda yake yi wa maƙwabcinsa daɗin baƙi yana kafa wa kansa tarko.


Masu son kashe ni, sun haƙa mini tarkuna, Masu so su cuce ni, suna barazanar lalatar da ni, Yini sukutum suna ƙulla mini maƙarƙashiya.


Sai Saul ya umarci fādawansa, ya ce, “Ku yi magana da Dawuda a ɓoye, ku ce masa, ‘Ga shi, sarki yana jin daɗinka, dukan fādawansa kuma suna ƙaunarka, yanzu sai ka zama surukin sarki.’ ”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ