1 Samaʼila 18:17 - Littafi Mai Tsarki17 Sai Saul ya ce wa Dawuda, “Ga Merab babbar 'yata, zan ba ka ita ka aura, idan ka yi mini aikin jaruntaka, wato ka yi yaƙin Ubangiji.” (Gama Saul yana tsammani ta wannan hanya Filistiyawa za su kashe Dawuda, ba lalle sai shi da kansa ya kashe shi ba.) အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202017 Shawulu ya ce wa Dawuda, “Ga diyata Merab zan ba ka ka aura, kai dai ka yi mini aiki da himma, ka kuma yi yaƙe-yaƙen Ubangiji.” Saboda Shawulu ya ce wa kansa, “Ba zan ɗaga hannuna a kansa ba, Filistiyawa ne za su yi wannan.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |