1 Samaʼila 18:13 - Littafi Mai Tsarki13 Saboda haka Saul bai yarda Dawuda ya zauna tare da shi ba, amma ya maishe shi shugaban dubu. Shi kuwa ya riƙa bi da su cikin kai da kawowa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202013 Saboda haka Shawulu bai yarda Dawuda yă zauna tare da shi ba, amma ya maishe shi shugaban sojoji dubu. Dawuda kuwa ya riƙa bi da su yana kaiwa yana kuma da tare da su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai ya ce wa fādawan da suke tsaye kewaye da shi, “Ku ji, ya ku mutanen Biliyaminu, ɗan Yesse zai ba kowannenku gonaki, da gonakin inabi ne? Zai maishe ku shugabanni na dubu dubu, da na ɗari ɗari, har da dukanku kuka yi mini maƙarƙashiya? Ba wanda ya sanar da ni sa'ad da ɗana ya haɗa kai da ɗan Yesse? Ba wanda ya damu saboda da ni, balle a faɗa mini yadda ɗana ya kuta barana ya tayar mini, yana fakona, kamar yadda yake a yau?”