56 Sai ya ce, “Ka tambaya mini, wane ne uban saurayin nan.”
56 Sarki ya ce, “Ka tambaya mini ko yaron wane ne wannan saurayi.”
Sa'ad da Saul ya ga Dawuda ya tafi ya yi yaƙi da Goliyat, ya ce wa Abner, sarkin yaƙinsa, “Abner, ɗan wane ne wannan saurayi?” Abner ya amsa, ya ce, “Ranka ya daɗe, ya sarki, ban sani ba.”
Da Dawuda ya komo daga kisan Goliyat, sai Abner ya kai shi wurin Saul, Dawuda yana ɗauke da kan Bafilisten.
Saul ya ce wa Dawuda, “Ba za ka iya yaƙi da wannan Bafiliste ba, gama kai ɗan saurayi ne, shi kuwa ya saba da yaƙi tun yana saurayi.”