Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 17:51 - Littafi Mai Tsarki

51 Sa'an nan ya sheƙa zuwa wurin Bafilisten, ya zare takobin Bafilisten daga kubensa, ya datse masa kai da shi. Da Filistiyawa suka ga jaruminsu ya mutu, sai suka gudu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

51 Dawuda ya ruga ya tsaya a bisan Bafilistin, ya zare takobin Bafilistin daga kubensa, ya datse masa kai da shi. Da Filistiyawa suka ga jaruminsu ya mutu, sai suka juya suka gudu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 17:51
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

suka i, wa ikon wuta, suka tsere wa kaifin takobi, suna marasa ƙarfi sai suka zama masu ƙarfi, suka yi jaruntaka a wajen yaƙi, suka fatattaka rundunar waɗansu ƙasashe.


Firist ya ce, “Ga takobin Goliyat, Bafiliste wanda ka kashe a kwarin Ila, a naɗe da zane a bayan falmaran. Idan kana so ka ɗauka, sai ka ɗauka, gama banda shi, ba wani takobi a nan.” Dawuda kuwa ya ce, “Ai, ba wanda ya fi wannan, sai ka ba ni shi.”


Ya kuma kashe wani Bamasare mai cika fuska. Bamasaren yana da māshi a hannunsa, amma Benaiya ya tafi wurinsa da sanda, ya fizge mashin daga hannun Bamasaren, ya kashe shi da māshin.


Wato tun da yake 'ya'yan duk suna da nama da jini, shi ma sai ya ɗauki kamannin haka, domin ya hallakar da mai ikon mutuwa, wato iblis, ta wurin mutuwarsa,


Aka kuwa rataye Haman a gungumen itace da ya shirya zai rataye Mordekai. Sa'an nan sarki ya huce.


Da majajjawa da dutse kawai Dawuda ya ci nasara da Bafilisten. Ya buge shi, ya kashe shi ba tare da takobi a hannunsa ba.


Sai Dawuda ya tashi, yana gudu ke nan daga wurin Saul. Ya tafi wurin Akish, Sarkin Gat.


Suka yanke kansa, suka tuɓe makamansa. Suka aika manzannin a ƙasar Filistiyawa da suke kusa don su kai wannan albishir zuwa ga haikalin gumakansu, da mutanensu.


Da suka shiga gidan, sai suka iske shi yana kwance a ɗakin kwanansa. Suka buge shi, suka kashe shi, suka datse kansa. Suka ɗauki kansa suka bi ta hanyar Araba, suka yi tafiya dare farai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ