Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 17:46 - Littafi Mai Tsarki

46 A yau Ubangiji zai bashe ka a hannuna, zan buge ka har ƙasa, in datse kanka, in ba da gawawwakin rundunar Filistiyawa ga tsuntsayen sama da namomin jeji, da haka duniya za ta sani lalle akwai Allah cikin Isra'ila.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

46 Yau nan, Ubangiji zai bashe ka a hannuna, zan kuwa kashe ka, in datse kanka. Yau, zan ba da gawawwakin rundunar Filistiyawa ga tsuntsayen sama da namun jeji, da haka duniya za tă sani lalle akwai Allah a cikin Isra’ila.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 17:46
30 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji ya nuna ikonsa mai tsarki, Ya ceci jama'arsa, Dukan duniya kuwa ta gani.


domin dukan mutanen duniya su sani Ubangiji yana da iko, domin kuma ku kasance da tsoron Ubangiji Allahnku har abada.”


Yanzu ya Ubangiji Allahnmu, ina roƙonka ka cece mu daga hannunsa domin dukan mulkokin duniya su sani kai kaɗai ne Allah, ya Ubangiji.”


sai ka kasa kunne ga addu'arsa. Ka ji daga Sama, wurin zamanka, ka amsa masa abin da ya roƙe ka, domin dukan mutanen duniya su san sunanka, su kuma yi tsoronka kamar jama'arka, Isra'ilawa, domin kuma su sani wannan Haikali da na gina wurin da za a yi maka sujada ne.


Gawawwakinku za su zama abinci ga dukan tsuntsayen sama, da namomin duniya. Ba wanda zai kore su.


Ya kuma ce wa Daniyel, “Hakika, Allahnka, Allahn alloli ne da Ubangijin sarakuna, mai bayyana asirai, gama ka iya bayyana wannan asiri.”


Amma na bar ka ka rayu domin in nuna maka ikona, domin kuma sunana ya zama abin darajantawa a dukan duniya.


Inda mushe yake, ai, a nan ungulai sukan taru.


Domin haka ina ba da wannan umarni cewa, ‘Dukan jama'a, ko al'umma, ko harshe wanda zai yi saɓon Allah na Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, za a yanyanka su gunduwa gunduwa, a ragargaje gidajensu, gama ba wani allah wanda zai yi wannan irin ceto.’ ”


Yanzu dai, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga Assuriyawa domin dukan al'umman duniya su sani kai ne Allah kai kaɗai.”


Ya ce, “Ku yi shiru, ku sani ni ne Allah, Maɗaukaki ne cikin sauran al'umma, Maɗaukaki kuma a duniya!”


Ya kuma ce wa Dawuda, “Ya ka nan, ni kuwa in ba da namanka ga tsuntsayen sama da namomin jeji.”


Ubangiji Allahnku zai bashe su a gare ku, zai firgitar da su har ya hallakar da su.


Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya bashe su a hannunku, kuka kuma ci nasara a kansu, sai ku hallaka su sarai. Kada ku yi alkawari da su, kada kuma ku yi musu jinƙai.


Dukanku namomin jeji ku zo ku ci, dukanku namomin jeji.


Ba ka bar magabtana su kama ni ba, Ka kiyaye ni.


Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “Kada ka ji tsoronsu gama na riga na ba da su a hannunka, ba mutuminsu da zai iya tsayawa a gabanka.”


Jonatan ya ce wa saurayin da yake ɗaukar masa makamai, “Zo, mu haye zuwa sansanin marasa kaciyan nan, arnan nan, watakila Ubangiji zai yi aiki ta wurinmu, gama ba abin da zai hana Ubangiji ya yiwo ceto ta wurin masu yawa, ko kuwa ta wurin 'yan kaɗan.”


Da Ahimawaz ya zo kusa da sarki, ya ce, “Salama!” Sa'an nan ya rusuna a gaban sarki ya sunkuyar da fuska ƙasa, ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka, wanda ya ba da mutanen da suka tayar wa ubangijina, sarki.”


Rizfa kuwa, 'yar Aiya, ta ɗauki algarara ta yi wa kanta shimfiɗa a kan dutsen. Ta zauna a wurin tun daga farkon kaka har zubar ruwan damuna da ya bugi gawawwakin. Ba ta bar tsuntsaye su sauka a kansu da rana ba, ko namomin jeji da dare.


domin dukan al'umman duniya su sani Ubangiji shi kaɗai ne Allah, banda shi, ba wani.


Ya kuwa komo wurin annabi Elisha shi da jama'arsa duka, ya zo ya tsaya a gabansa, ya ce, “Yanzu na sani a duniya duka ba wani Allah banda na Isra'ila, saboda haka, sai ka karɓi kyauta daga wurina.”


zan bashe su a hannun abokan gabansu waɗanda suke neman ransu. Gawawwakinsu za su zama abincin tsuntsaye da namomin jeji.


bayan kwana uku Fir'auna zai falle kanka ya rataye ka a bisa itace, tsuntsaye kuwa za su ci naman jikinka.”


A wannan wuri zan wofinta dabarun Yahuza da na Urushalima, zan sa a kashe jama'arsu da takobi, a gaban abokan gābansu, ta hannun waɗanda suke neman ransu. Zan ba da gawawwakinsu su zama abincin tsuntsayen sararin sama da na namomin jeji.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ