Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 17:34 - Littafi Mai Tsarki

34 Amma Dawuda ya ce wa Saul, “Ai, baranka makiyayin tumakin mahaifinsa ne, sa'ad da zaki ko beyar ya zo ya kama ɗan rago daga garken,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

34 Amma Dawuda ya ce wa Shawulu, “Bawanka yana kiwon tumakin mahaifinsa. Sa’ad da zaki ko beyar ta zo ta kama tunkiya, ta tafi da ita.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 17:34
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

waɗanda ta wurin bangaskiya suka ci masarautai, suka aikata adalci, suka sami cikar alkawarai, suka rurrufe bakunan zakoki,


Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko a kansa da iko, sai ya yaga zakin da hannu, kamar yadda akan yayyage ɗan akuya. Amma bai faɗa wa iyayensa abin da ya yi ba.


Saul ya ce wa Dawuda, “Ba za ka iya yaƙi da wannan Bafiliste ba, gama kai ɗan saurayi ne, shi kuwa ya saba da yaƙi tun yana saurayi.”


nakan bi shi in fāɗa masa, in ƙwato ɗan ragon daga bakinsa. Idan ya tasar mini da faɗa, sai in kama reronsa, in buge shi, in kashe shi.


Ubangiji ya ce, “Kamar yadda makiyayi yakan ceci ƙafafu biyu Ko kunne ɗaya na tunkiya daga bakin zaki, Haka nan kuma kima daga cikin mutanen Samariya Waɗanda suke zaman jin daɗi za su tsira.


Wanda namomin jeji suka yayyaga ban kawo maka ba, ni da kaina na ɗauki hasararsu. Ka kuma nemi abin da aka sace da rana ko da dare daga hannuna.


Dawuda yakan koma Baitalami lokaci lokaci domin kiwon tumakin mahaifinsa.


Hushai ya ci gaba da cewa, “Ka san tsohonka da jama'arsa jarumawa ne, yanzu a husace suke kamar damisar da aka kwashe wa 'ya'ya a jeji. Tsohonka kuma ya ƙware da sha'anin yaƙi, ba tare da mutanensa zai kwana ba.


Benaiya ɗan Yehoyada, mutumin Kabzeyel, jarumi ne. Ya yi manyan ayyuka. Ya kashe ƙwararrun jarumawa biyu na Mowab. Wata rana kuma da aka yi dusar ƙanƙara, sai ya tafi ya kashe zaki a kogo.


Benaiya ɗan Yehoyada, ɗan wani jarumi ne daga Kabzeyel, ya yi manyan ayyuka, ya kashe jarumawa biyu na Mowabawa. Sai ya gangara ya kashe zaki a cikin rami a ranar da ake yin dusar ƙanƙara.


Na tuna kwanakin baya, Na tuna da dukan abin da ka yi, Na tuna da dukan ayyukanka.


Kamar yadda makiyayi yakan nemo tumakin da suka watse daga cikin garkensa, haka zan nemi tumakina. Zan cece su daga dukan wuraren da aka watsar da su a ranar gizagizai da baƙin duhu.


Zan kawar da jininsu daga bakinsu, Da kuma haramtattun abubuwa daga haƙoransu. Sauransu za su zama jama'ar Allahnmu, Za su zama kamar sarki cikin Yahuza. Mutanen Ekron za su zama kamar Yebusiyawa.


Gama ga shi, zan sa wani makiyayi a ƙasan nan, wanda ba zai kula da masu lalacewa ba, ko waɗanda suka warwatse, ko ya warkar da gurgu, ko ya ciyar da waɗanda suka ragu, amma zai ci naman masu ƙiba, ya farfashe kofatonsu.


A wannan yankin ƙasa kuwa waɗansu makiyaya suna kwana a filin Allah, suna tsaron garken tumakinsu da dad dare.


Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau kuwa shi ne mai ba da ransa domin tumakin.


jimiri kuma yake sa ingataccen hali, ingataccen hali kuma yake sa sa zuciya,


Dabbar da na gani kuwa kamar damisa take, ƙafafunta kamar na beyar, bakinta kuma kamar na zaki. Macijin kuwa ya ba ta ƙarfinsa, da kursiyinsa, da ikonsa mai girma.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ