Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 17:33 - Littafi Mai Tsarki

33 Saul ya ce wa Dawuda, “Ba za ka iya yaƙi da wannan Bafiliste ba, gama kai ɗan saurayi ne, shi kuwa ya saba da yaƙi tun yana saurayi.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

33 Shawulu ya ce, “Ba za ka iya yin faɗa da wannan Bafilistin ba, ya daɗe yana yaƙi, ya yi yaƙi tun yana saurayi. Ga shi kuwa kai ɗan yaro ne kawai.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 17:33
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai mutanen da suka tafi tare da shi suka amsa suka ce, “Ba za mu iya haurawa, mu kara da mutanen ba, gama sun fi mu ƙarfi.”


har suka yi wa macijin nan sujada, don shi ne ya bai wa dabbar ikonsa, suka kuma yi wa dabbar sujada, suna cewa, “Wa ya yi kama da dabbar nan? Wa kuma zai iya yaƙi da ita?”


Mutane ne ƙarfafa, dogaye, zuriyar Anakawa waɗanda kuka riga kuka ji labarinsu. Ai, kun ji akan ce, ‘Wane ne zai iya tsayayya da 'ya'yan Anak?’


Na dogara ga Ubangiji domin zaman lafiya, Wauta ce idan kun ce mini, “Ka yi firiya kamar tsuntsu zuwa duwatsu,


Sai ya ce, “Ka tambaya mini, wane ne uban saurayin nan.”


Sa'ad da ya ga Dawuda, sai ya raine shi, gama Dawuda saurayi ne kawai, kyakkyawa.


Amma Dawuda ya ce wa Saul, “Ai, baranka makiyayin tumakin mahaifinsa ne, sa'ad da zaki ko beyar ya zo ya kama ɗan rago daga garken,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ