27 Mutane suka maimaita masa abin da sarki ya faɗa.
27 Sai suka sāke gaya masa abin da suka faɗa cewa, “Ga abin da zai faru da wanda ya kashe shi.”
Suka ce, “Kun ga mutumin nan da ya fito? Lalle ya fito ne don ya nuna mana raini. Duk wanda ya kashe shi, sarki zai arzutar da shi, ya ba shi 'yarsa aure, ya kuma 'yantar da gidan mahaifinsa cikin Isra'ila.”
Sai ya rabu da shi ya tafi wurin wani, ya sāke yin tambaya irin ta dā, mutane kuma suka ba shi amsa irin ta dā.