Kashegari sai Dawuda ya tashi tun da sassafe, ya bar tumaki a hannun wani makiyayi, ya ɗauki guzurin, ya tafi kamar yadda mahaifinsa, Yesse, ya umarce shi. Ya isa sansani daidai lokacin da runduna suke fita tana kirari na jān dāgar yaƙi.
Sunan mutumin, Elimelek, matarsa kuwa Na'omi, 'ya'yanta maza kuma Malon da Kiliyon. Su Efratawa ne daga Baitalami ta Yahudiya. Suka tafi Mowab suka zauna a can.