Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 17:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Kashegari sai Dawuda ya tashi tun da sassafe, ya bar tumaki a hannun wani makiyayi, ya ɗauki guzurin, ya tafi kamar yadda mahaifinsa, Yesse, ya umarce shi. Ya isa sansani daidai lokacin da runduna suke fita tana kirari na jān dāgar yaƙi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Kashegari da sassafe, Dawuda ya tashi ya bar tumakinsa wa wani yă lura da su, sai ya ɗauki kayansa, ya kama hanya kamar yadda Yesse ya umarce shi. Ya isa sansanin daidai sa’ad da rundunar tana fitowa zuwa bakin dāgā, suna kirarin yaƙi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 17:20
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Don lokaci zai auko muku da maƙiyanku za su yi muku ƙawanya, su yi muku zobe, su kuma tsattsare ku ta kowane gefe,


Dawuda kuwa ya tashi ya tafi wurin da Saul ya kafa sansani. Ya kuwa ga inda Saul yake kwance, da kuma Abner ɗan Ner, sarkin yaƙin Saul. Saul ya kwanta a sansanin, sojojin suna kewaye da shi.


Sai Dawuda da Abishai, suka tafi sansanin Saul da dare. Suka tarar da Saul yana barci cikin sansani da mashinsa a kafe a ƙasa, wajen kansa. Abner kuwa da sauran sojoji suna kwance kewaye da shi.


Lokacin da Dawuda yake magana da mutanen, sai Eliyab babban wansa ya ji, ya husata, ya ce wa Dawuda, “Me ya kawo ka nan? Wa ka bar wa 'yan tumakin nan a jeji? Na san rigimarka da taurinkanka, ka zo ne don ka yi kallon yaƙi.”


Da Saul, da 'yan'uwanka, da dukan mazajen Isra'ila suna kwarin Ila, suna yaƙi da Filistiyawa.”


Isra'ilawa da Filistiyawa suka jā dāga, runduna gāba da runduna.


Joshuwa kuwa ya tashi da sassafe, da shi da dukan jama'ar Isra'ila, suka kama hanya daga Shittim zuwa Urdun, inda suka sauka kafin su haye.


Sa'an nan ya tashi tun da sassafe domin ya sadu da Saul. Aka faɗa wa Sama'ila, Saul ya tafi Karmel, ya kafa wa kansa al'amudi, sa'an nan ya juya ya wuce zuwa Gilgal.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ