Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 17:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Dawuda kuwa ɗan Yesse ne, wanda yake mutumin Efrata, ta Baitalami cikin Yahuza, yana da 'ya'ya maza guda takwas, ya kuwa riga ya tsufa a zamanin Saul.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 To, Dawuda dai ɗan wani mutumin Efratawa ne mai suna Yesse, shi mutumin Betlehem ne a cikin Yahudiya. Yesse yana da yara maza takwas, a zamanin Shawulu kuwa, Yesse ya riga ya tsufa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 17:12
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ta haka fa Rahila ta rasu, aka kuwa binne ta a bakin hanya zuwa Efrata, wato Baitalami.


Sai wani daga cikin samarin ya amsa, ya ce, “Na san wani ɗan Yesse mutumin Baitalami. Shi gwanin kiɗan garaya ne, jarumi ne kuma, mayaƙi, mai lafazi, kyakkyawa, Ubangiji kuwa yana tare da shi.”


Saul ya tambayi Dawuda, ya ce, “Saurayi, kai ɗan wane ne?” Dawuda ya amsa, ya ce, “Ni ɗan baranka ne, Yesse, mutumin Baitalami.”


“ ‘Ke ma Baitalami, ta kasar Yahuza, Ko kusa ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin manyan garuruwan Yahuza ba, Domin daga cikinki za a haifi wani mai mulki, Wanda zai zama makiyayin jama'ata, Isra'ila.’ ”


Yesse ya haifi sarki Dawuda. Dawuda kuma ya haifi Sulemanu (wanda uwa tasa dā matar Uriya ce),


Ubangiji ya ce wa Sama'ila, “Har yaushe za ka yi ta ɓacin rai saboda Saul? Ga shi kuwa, na ƙi shi da zama Sarkin Isra'ila. Ka sami man zaitun ka ɗauka. Zan aike ka zuwa wurin Yesse mutumin Baitalami, gama na zaɓi ɗaya daga cikin 'ya'yansa maza ya zama sarki.”


Sa'ad da aka haifi Yesu a Baitalami ta ƙasar Yahudiya, a zamanin sarki Hirudus, sai ga waɗansu masana taurari daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa,


“Baitalami cikin Efrata, Wadda kike 'yar ƙarama a cikin kabilar Yahuza, Amma daga cikinki wani zai fito wanda zai sarauci Isra'ila Wanda asalinsa tun fil azal ne.”


Mun ji labari akwatin alkawari yana Baitalami, Amma muka same shi a kurmi.


Sa'ad da Saul da dukan Isra'ilawa suka ji maganganun da Bafilisten nan yake faɗa, sai suka karaya, suka tsorata ƙwarai.


Sunan mutumin, Elimelek, matarsa kuwa Na'omi, 'ya'yanta maza kuma Malon da Kiliyon. Su Efratawa ne daga Baitalami ta Yahudiya. Suka tafi Mowab suka zauna a can.


Mata, maƙwabta kuwa suka ce, “An haifa wa Na'omi ɗa!” Suka raɗa masa suna Obida, shi ne mahaifin Yesse, uban Dawuda.


Akwai wani mutum daga kabilar Ifraimu sunansa Elkana, yana zaune a Rama, a ƙasar tudu ta Ifraimu. Shi ɗan Yeroham ne, jika ga Eliyab, na iyalin Nahat, daga zuriyar Zuf.


Wannan ita ce maganar Dawuda ta ƙarshe. Dawuda ɗan Yesse, shi ne mutumin da Allah ya ɗaukaka, wanda Allah na Yakubu ya zaɓa ya zama sarki, wanda kuma ya shirya waƙoƙin Isra'ila. Dawuda ya ce,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ