Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 17:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Sa'ad da Saul da dukan Isra'ilawa suka ji maganganun da Bafilisten nan yake faɗa, sai suka karaya, suka tsorata ƙwarai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Da jin maganganun Bafilistin, sai Shawulu da dukan Isra’ila suka damu suka kuma ji tsoro.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 17:11
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ashe, ban umarce ka ba? Ka dāge ka yi ƙarfin hali, kada ka firgita ko ka tsorata, gama Ubangiji Allahnka yana tare da kai duk inda za ka.”


Ubangiji kansa zai bi da kai, ba zai kunyatar da kai ba, ba kuwa zai yashe ka ba. Kada ka ji tsoro, kada kuma ka karai.”


Ubangiji ya ce, “Wa ya sa ku fargaba, kuke jin tsoronsa, har kuka yi ƙarya? Ba ku tuna da ni, ko ku kula da ni ba? Ashe, ban yi haƙuri tun da daɗewan nan ba, duk da haka kuwa ba ku ji tsorona ba?


Mugun mutum yakan gudu, alhali kuwa ba mai korarsa, amma amintaccen mutum kamar zaki yake, ba shi da tsoro.


Ubangiji ne haskena da cetona, Ba zan ji tsoron kowa ba. Ubangiji yana kiyaye ni daga dukan hatsari, Ba zan ji tsoro ba.


Da Filistiyawa suka ji Isra'ilawa sun taru a Mizfa, sai sarakunan Filistiyawa, su biyar, suka tafi, su yi yaƙi da Isra'ilawa. Sa'ad da Isra'ilawa suka ji labari, sai suka tsorata,


Ya ƙara da cewa, “Na raina rundunan Isra'ila yau. Ku ba ni mutumin da zan yi yaƙi da shi.”


Dawuda kuwa ɗan Yesse ne, wanda yake mutumin Efrata, ta Baitalami cikin Yahuza, yana da 'ya'ya maza guda takwas, ya kuwa riga ya tsufa a zamanin Saul.


Waɗansu kuwa suka haye Kogin Urdun zuwa ƙasar Gad da Gileyad. Saul kuwa yana can a Gilgal. Dukan mutanen da suka bi shi suka yi ta rawar jiki.


Ya mai da kansa kamar mahaukaci a gabansa. Ya yi zane-zane a ƙyamaren ƙofofin garin. Ya bar yau na bin gemunsa.


Ubangiji yana tare da ni, ba zan ji tsoro ba. Me mutane za su iya yi mini?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ