Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 16:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Ka gayyaci Yesse zuwa wurin hadayar, zan nuna maka abin da za ka yi. Za ka zuba wa wanda na nuna maka mai.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Ka gayyato Yesse a wurin hadayar, ni kuma zan gaya maka abin da za ka yi. Za ka shafe mini wanda na nuna maka.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 16:3
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya ce masa, “Gobe war haka zan aiko maka da wani mutum daga kabilar Biliyaminu, sai ka zuba masa mai, ka keɓe shi sarki bisa jama'ata Isra'ila. Zai ceci jama'ata daga hannun Filistiyawa, gama na ga azabar da jama'ata suke sha, gama na ji kukansu.”


Amma ka tashi ka shiga gari, can za a faɗa maka abin da za ka yi.”


Mutum metan waɗanda ya gayyata daga Urushalima suka tafi tare da shi da zuciya ɗaya ba tare da sanin kome ba.


Sai ka yi magana da shi. Ka kuma sa masa maganata a baka, zan kuwa kasance tare da bakinka da bakinsa. Zan kuma sanar da ku abin da za ku yi.


a can Zadok firist, da annabi Natan za su zuba masa mai, ya zama sarkin Isra'ila, sa'an nan ku busa ƙaho, ku ce, ‘Ran sarki Sulemanu ya daɗe.’


Sai dattawan Isra'ilawa suka zo wurin sarki Dawuda a Hebron. Dawuda kuwa ya yi alkawari da su a Hebron a gaban Ubangiji, ake kuwa naɗa Dawuda ya zama Sarkin Isra'ila bisa ga faɗar Ubangiji ta bakin Sama'ila.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ