1 Samaʼila 14:6 - Littafi Mai Tsarki6 Jonatan ya ce wa saurayin da yake ɗaukar masa makamai, “Zo, mu haye zuwa sansanin marasa kaciyan nan, arnan nan, watakila Ubangiji zai yi aiki ta wurinmu, gama ba abin da zai hana Ubangiji ya yiwo ceto ta wurin masu yawa, ko kuwa ta wurin 'yan kaɗan.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20206 Yonatan ya ce wa saurayin mai ɗaukan makamai, “Zo mu haye zuwa mashigin mutane marasa kaciyan nan, wataƙila Ubangiji zai yi aiki a madadinmu. Ba abin da zai iya hana Ubangiji yin aikin ceto ta wurin mutane masu yawa, ko ta wurin mutane kaɗan.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Asa kuwa ya yi kuka ga Ubangiji Allahnsa, ya ce, “Ya Ubangiji, ba wani mai taimako kamarka, wanda zai yi taimako sa'ad da mai ƙarfi zai kara da marar ƙarfi, ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama a gare ka muke dogara, da sunanka kuma muka zo don mu yi yaƙi da wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu, kada ka bar mutum ya rinjayi jama'arka.”