Saul ya ce, “Ni mutumin kabilar Biliyaminu ne, kabilar da ta fi ƙanƙanta a Isra'ila. Iyalina kuma su ne mafi ƙanƙanta a iyalan kabilar Biliyaminu. Me ya sa ka faɗa mini irin wannan magana?”
Dawuda kuwa ya tashi ya tafi wurin da Saul ya kafa sansani. Ya kuwa ga inda Saul yake kwance, da kuma Abner ɗan Ner, sarkin yaƙin Saul. Saul ya kwanta a sansanin, sojojin suna kewaye da shi.