1 Samaʼila 14:45 - Littafi Mai Tsarki45 Amma jama'a suka ce wa Saul, “Jonatan da ya yiwo babbar nasara domin Isra'ila, a ce za a kashe shi? Kai, a'a! Mun yi alkawari ga Ubangiji mai rai, Jonatan ba zai yi hasarar ko gashi guda daga kansa ba. Abin da ya yi a yau, da taimakon Allah ne ya yi.” Da haka mutane suka ceci Jonatan, har ba a kashe shi ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202045 Amma mutane suka ce wa Shawulu, “A ce Yonatan yă mutu bayan shi ya kawo babban nasara a Isra’ila? Faufau, muddin Ubangiji yana raye, ko gashin kansa ɗaya ba zai fāɗi a ƙasa ba, gama abin da ya yi yau, Allah ne yana tare da shi.” Ta haka mutane suka ceci Yonatan daga mutuwa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Amariya, babban firist, shi ne zai shugabance ku a kan dukan al'amuran da suke na wajen Ubangiji. Zabadiya, ɗan Isma'ilu mai mulkin gidan Yahuza, shi ne shugabanku a kan dukan al'amuran da suke na wajen sarki. Lawiyawa kuwa su zama muhimman ma'aikatanku. Kada ku ji tsoro a cikin aikinku, Ubangiji kuwa ya kasance tare da masu gaskiya.”